Majalisar Musulmi a Kasar Ingila ta gudanar da za?en Shugabannin ta da zasu ja ragamar majalisar, inda suka zabi Malama Zara Muhammad a matsayin Shugabar Majalisar.
Zara Mohammed ta ce tana fatan za?enta a matsayin Sakatare Janar na Majalisar Musulmai ta Birtaniya zai zama ?warin guiwa ga mata da matasa su kai ga matsayi na shugabanci.
Masaniya dokokin kare hakkin dan adam ce. Za ta yi wa’adin shugabanci na shekara biyu.
An kafa majalisar ne a 1997 kuma ta ?unshi masallatai 500 da makarantu da ?ungiyoyin musulmai.
Sai dai a hannu guda jama’a na cigaba da bayyana ra’ayoyin su akan wannan za?e da majalisar Musulmin Amurka ta yi, inda wasu jama’a ke sukar matakin da ganin ya yi hannun riga da karantarwar addinin Musulunci.