Ƙetare: Biden Ya Soke Takunkumin Da Trump Ya Ƙaƙaba Wa Musulmi

Yayin da ake dakon rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka a ranar Laraba, tawagar zababben shugaban ta bayyana jerin dokokin da Trump ya sanya da yake shirin sokewa a ranar da aka rantsar da shi.

Shugaban ma’aikata na Mista Biden Ron Klain ya ce da zarar an rantsar da Biden, zai mayar da Amurka cikin yarjejeniyar sauyin yanayi, sannan ya soke haramcin shiga kasar daga wasu kasashen musulmai da shugaba Trump ya sanya.

Yanzu haka dai yawan dakarun da aka jibge a birnin Washington domin tabbatar da an yi bikin rantsuwar lafiya ya ninninka yawan dakarun kasar a kasashen Afghanistan da Iraqi.

Dukkanin jihohin Amurka 50 da Gundumar Columbia na cikin shirin ko ta kwana saboda yiwuwar samun zanga-zanga a karshen makon nan, gabanin bikin rantsar da sabon shugaban kasar Joe Biden a ranar Laraba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply