Ƙetare: Belgium Ta Kori Mutanen Da Suka Yi Yunƙurin Ƙona Al-Kur’ani

Wasu ‘Yan ƙasar Denmark da ake zargin suna kokarin fusata Musulman kasar Belgium ta hanyar kona Al-Kur’ani sun shiga hannu kuma an fitar da su daga kasar ba tare da ɓata lokaci ba.

A labarin da aka daura a shafin kungiyar ta Facebook, wadanda aka kama mambobin kungiyar “Stram Kurs” ne – wata kungiyar yan kasar Denmark masu yaki da Musulunci da kuma yan gudun Hijra karkashin jagorancin Rasmus Paludan.

A cewar shafin, an damke Paludan da kansa a kasar Faransa kuma an fitattakeshi.

Kungiyar Stram Kurs ta shahara wajen yin abubuwan tayar da zaune tsaye kuma hukumomin kasar Belgium sun samu labarin sun shirya bikin kona Al-Kur’ani a Molenbeek, wani gari da ke da adadin ‘Yan kasar Maroko da yawa.

Wata majiya ta bayyanawa AFP cewa an sanarwa ‘yan sanda shirye-shiryen da suke yi, kuma nan take aka ɗauki matakin kariya.

Sakataren harkokin wajen Belgium Misra Sammy ya yi na’am da damke wadannan mutane biyar. “An umurcesu su fita daga kasar ba tare da bata lokaci ba, kuma sun yi hakan,”

“An hana su zama saboda kasancewarsu a kasar Belgium matsala ne ga al’umma. An damke wani mutum a Faransa ta wannan dalili.” “Har da kasar jamus ta dauki irin wannan mataki kan wannan mutum (shugabansu), saboda jami’an tsaro sun dauke shi mai yada da’awar kiyayya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply