Dubun dubatar mutane sun yi zanga-zanga a babbar birnin Senegal, Dakar, ranar Asabar kan zanen batancin da akayi wa manzon Allah (SAW) da kuma kare hakan da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ke yi.
Jaridan AFP ta ruwaito masu zanga-zangar suna kona tutocin kasar Faransa da hotunan shugaban kasan kuma suna kira ga kauracewa kayayyakin kasar Faransa a kasashen Musulmai.
“Macron ya jiwa Musulman duniya rauni. Idan duniya ta zauna lafiya, aikin addinin Islama ne. Na ki jinin Macron,” wani mai zanga-zanga Youssoupha Sow, yace.
Zanga-zanga ta barke sassa daban daban na kasashen duniya bayan kalaman shugaban kasar Faransa, inda ya lashi takobin fito-na-fito da Musulunci da kuma kare masu zanen batanci ga manzon Allah.
Kashi 95% na jama’ar kasar Senegal Musulmai ne kuma ƙasar Faransa tayi musu mulkin mallaka tare da basu yancin kai.
Daya daga cikin masu zanga-zangan Marcer Awa Thiam yace: “Ba wai muna yaki Faransa bane. kawai muna son ‘yan’uwanmu Musulmai su yi addininsu cikin kwanciyan hankali.”
“Bai kamata ana ba mutane tsoro ba, cewa addinin Musulunci addinin ta’addanci ne ko mugunta… maganar gaskiya itace babu addini mafi zaman lafiya kaman Musulunci.”
Wani mai zanga-zangan, Kara Sow yace “Muna son Manzon Allah fiye da iyayenmu.”