Ƙetare: An Yankewa Trump Da Sarki Salman Hukuncin Kisa

Wata kotu a kasar Yemen ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutum 10 ciki har da Shugaba Donald Trump, Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Yarima Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud saboda aikata laifukan yaki.

An yanke hukuncin ne a wata Kotu ta musamman ta masu manyan laifuka, biyo bayan harin hadin gwiwa da aka kai wa wata motar bas cike da kananan yara a mazaɓar Majz take Yemen.

Amma wadanda aka yanke wa hukuncin ba su hallarci zaman shari’ar ba a kotun na ‘yan Houthi kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Kafar watsa labarai mallakar Houthi a Yemen, SABA, ta tabbatar da yanke hukuncin kisar da aka yi wa Donald Trump, Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, Mohammed Bin Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, da Norton Schwartz saboda hannunsu a kai harin.

Sauran wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Kwamandan Sojin Saman Saudiyya, Turki bin Bandar bin Abdulaziz, Shugaban kasar Yemen Abedrabbo Mansour Hadi, mataimakin shugaban kasar Yemen Ali Mohsen Saleh Al-Ahmar.

Ministan Tsaro Muhammad Al-Maqdishi, da tsohon sakataren tsaro na Amurka James Norman Mattis suma duk an yanke musu hukuncin kisar.

Kafar watsa labaran ta kuma ruwaito cewa kotun ta bukaci wadanda aka yi kararsu su biya iyalan yaran da aka kashe a harin saman na shekarar 2019 tarar Dalan Amurka Biliyan 10.

Har wa yau, kafar watsa labaran ta ce wadanda aka yanke wa hukuncin suna da damar daukaka kara.

Labarai Makamanta