Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

?etare: An Rantsar Da Biden A Matsayin Za?a??en Shugaban Amurka

Joe Biden ya shafe shekara 50 a fagen siyasa inda yake ?o?ari ya ga ya cimma wannan burin, sai dai bai ta?a tsammanin zai tarar da irin wannan ?alubalen a gabansa ba.

Wa?anne abubuwa zai fi mayar da hankali a kai?

Zai shafe kusan kwanaki goma yana dokoki na musamman da ?arfin shugaban ?asa ya ba sa iko.

Irin wa?annan dokokin ba su bu?atar amincewar majalisar tarayya.

Cikin manyan abubuwan da ke cikin jerin abubuwan da Biden ?in zai mayar da hankali akwai batun haramcin da gwamnatin Trump ya saka wa wasu ?asashen Musulmi na shiga Amurka inda Shugaba Trump ya ce ?asashen barazana ne ga tsaron Amurka.

Haka kuma Mista Biden ?in zai mayar da hankali kan batun yarejejeniyar sauyin yanayi ta Paris.

Ga sauran abubuwan da ake sa ran Biden ?in zai mayar da hankali a kansu bayan an rantsar da shi.

Ya?i da annobar korona

Matakin saka takunkumi a Amurka
Annobar korona ta kashe sama da mutum 400,000 a Amurka – ana sa rai cewa annobar korona da kuma tasirinta ne muhimmin abin da gwamnatin Biden za ta mayar da hankali a kai.

Mista Biden ya ce annobar ce “ya?i mai muhimmanci da gwamnatinmu za ta fuskanta” kuma shugaban ya yi al?warin aiwatar da sabon tsarinsa na ya?i da korona nan take.
?aya daga cikin matakan nasa akwai batun saka takunkumi a duk wani wuri mallakar gwamnatin tarayya haka kuma a duk lokacin da ake tafiye-tafiye tsakanin jihohi.

Sai dai har yanzu babu wani tabbaci kan cewa gwamnonin jihohin Amurka wa?anda akasarinsu ke sukar matakin saka takunkumi za su sauya ra’ayinsu kan lamarin – haka kuma babu wata doka da ta bai wa shugaban ?asa ikon tilasta saka takunkumi a duka ?asa.

Da alama Mista Biden ya gane hakan inda ya bayyana cewa da kansa zai yi ?o?ari wajen ganin cewa ya shawo kan gwamnoni kan wannan lamari.

Idan gwamnonin ba su amince ba, ya sha alwashin zai yi kira ga magaddai da jami’an birane su rungumi wannan tsarin nasa. Babu tabbaci har yanzu kan yadda za a aiwatar da wannan tsari.

Rigakafi miliyan 100 a kwana 100

Mista Biden na so ya gaggauta yin riga-kafi a Amurka inda yake da burin tabbatar da cewa an yi wa mutum miliyan 100 a cikin kwana 100 na farko da zai yi kan mulki.

?aya daga cikin hanyoyin gaggauta yin riga-kafin ita ce ta fitar da duka riga-kafin da ake da su domin yi wa mutane a maimakon ajiye su ga wa?anda za a yi wa karo na biyu.

Ana kuma sa ran cewa shugaban zai ?auki matakin gaggawa na tabbatar da cewa an samar da hanyoyin gwajin korona cikin sauri da kuma samar da kayayyakin aiki da magunguna da kuma kayayyakin kariya.

Sake shiga Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO
Daga cikin abubuwan da ake tunanin Biden zai yi, akwai batun sauya matakin da Amurka ta ?auka a baya na barin Hukumar Lafiya Ta Duniya.

Mista Trump ya bayyana shirye-shiryen ficewa daga ?ungiyar ne a kwanakin baya inda yake zargin WHO ?in da gazawa wurin da?ile korona bayan ?ullarta daga China.

Dokoki na musamman da zai aiwatar – Ga wasu daga cikin sabbin dokokin da ake tunanin Biden zai aiwatar da zarar ya shiga ofis

Amurka za ta koma cikin yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi

Cire dokar da ta haramta wa wasu ?asashen Musulmi shiga Amurka

Tilasta saka takunkumi a wurare mallakar gwamnatin tarayya da kuma yayin tafiya tsakanin jihohi.

?ara wa’adin haya ga ?an haya da wa?anda ake bi basussuka sakamakon annobar korona

Ci gabada dakatar da biyan basussukan ?alibai a lokacin annobar

Matakan tattalin arzi?i

Sau?a?a wa ?an haya da masu gidaje

Kwamitin kamfe na Mista Biden ya bayyana cewa akwai shirye-shiryen da gwamnatin ke yi na tsawaita lokaci ga ?an haya da ke gidajen haya da wa?anda ake bi basussuka – haka kuma da batun dakatar da biyan bashin da ?aliban tarayya suke yi.

Kwamitin kar?ar mulki na Biden ya shaida cewa Biden ?in na ?o?arin fitar da shiri na musamman inda zai ba wasu ma’aikatu umarnin bayar da kayan agaji ga iyalai da ke aiki a ?asar, sai dai babu wani ?arin bayani kan irin abubuwan da za a bayar.

Tiriliyan $1.9 ga tattalin arzi?in Amurka
A makon da ya gabata ne Mista Biden ya sanar da cewa za a fitar da tiriliyan $1.9 domin bayar da tallafi ga mutanen ?asar sakamakon irin raunin da annobar korona ta yi wa tattalin arzi?in ?asar.

Idan majalisar tarayya suka amince da wannan ku?in, hakan zai ha?a da biyan dala 1,400 ga kowa a Amurka.

Haka kuma shugaban ya yi tsarin bai wa makarantu tallafin kudi domin su sake bu?ewa ba tare da wata matsala ba, haka kuma yana so makarantun su bu?e a cikin kwanaki 100 bayan kama aiki.

Hakan zai zama ?ari ga dala biliyan 900 na ku?in tallafi da majalisar ta amince a Disamban bara.

Da wuya ?an majalisa daga Jam’iyyar Republican su ?i amincewa da kudirin, wanda hakan zai zama ?ari ga bashin da Amurka ta kashe a ya?i da annobar korona, haka kuma Mista Biden zai bu?aci duka jam’iyyun biyu su ha?a kansu.

A yanzu dai ?an Democrats su ke da iko da duka majalisun biyu, amma da tazara ka?an.

Kawo ?arshen sabbin dokokin harajin da Trump ya sa

Ba bayar da tallafin Trump ne kawai abin da sabon shugaban ya sa a gaba ba. Ya yi al?awarin soke sauye-sauyen da Mista Trump ya yi a dokokin haraji.

Mista TRump ya yi sauyin ne a 2017, a farkon shugabancinsa kuma Biden ya ce ba a yi adalci ba musamman ga ?ananan masana’antu.

Haka kuma Biden ya ce zai ru?anya harajojin da kamfanonin Amurka su ke biya kan ribar da suka samu daga ?asashen waje.

Amma fa wannan ?udirin nasa zai bi ta hannun majalisa tukuna.

Muhalli da Sauyin Yanayi

Zai mayar da Amurka Yarjejeniyar Paris
Wani abu da Mista Biden ya ce zai yi a ranarsa ta farko a mulki shi ne komawa yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi, wata yarjejeniya da ta ?unshi tabbatar da tsare yanayi ?asa da 2.0c.

Trump ya janye Amurka ne daga yarjejeniyar a 2015, inda ta zama ?asa ta farko da ta yi haka.
Mista Biden ya ce yana so ya yi aiki da majalisar dokokin ?asar wajen sa dokar da za ta bai wa Amurka damar rage fitar da gur?atacciyar iska zuwa shekarar2050.

Soke dokokin sauyin yanayi

Wani abu kuma da sabon shugaban ya ce zai yi shi ne soke wasu manufofin sauyin yanayi da Trump ya kafa.

Mista Biden ya ce zai tattauana sosai kan gur?atacciyar iskar da motoci ke fitarwa da tsare kashi 30% na kasa da ruwan ?asar zuwa 2010, sannna zai rufe filin Arctic National Wildlife Refuge da ake ha?ar mai.

Sabuwar gwamnatin ta ce a shirye ta ke ta ta?aita fitar da iskar methane a yayin sarrafa man fetur da iskar gas.
Manufofin Ci Rani

Soke dokar shiga ?asar
Dokar da Mista TRump ya sa kwana bakawai bayan hawansa mulki a 2017 ta hana ?an wasu ?asar shiga Amurka na ?aya daga cikin dokokin da Biden zai soke.

Da farko dokar haramcin ta shafi wasu ?asashen Musulmi bakwai ne amma daga baya an yi sauye-sauye bayan da kotu ta sa baki a maganar.

A yanzu kasashen Iran da Libya da Somalia da Syriya da Yemen da Venezuela da Koriya ta Arewa ne ke ?ar?ashin dokar haramcin.

Za a sau?a?a wa ‘yan gudun hijira zama ?an ?asa

Wani babban al?awari da Mista Biden ya ?auka shi ne na gaggauta aikewa majalisa ?udirin doka da za ta bai wa ‘yan gudun hijira sama da miliyan 11 da ke zaune a ?asar damar zama ?an Amurka.

A lokacin ya?in neman za?ensa, Mista Biden ya ce zai kafa da kwamitin da zai ha?a yara ?an ci rani 545 da aka raba da iayyensu a iyakar Amurka.

A watan Disamba, tawagar Biden ta ce za ta bu?aci lokaci don ta soke ?aya daga cikin manufofin Mista Trump mai suna Migrant Protection Protocols da ta tursasa wa dubban masu neman mafaka a ?asar su jira a Mexico kafin kotuna a Amurka su saurari kokensu.
Jami’ai sun ce wannan na iya ?aukar wata shida.

Kawo ?arshen gina katanga

Mista Biden ya yi al?awarin tsayar da ginin katangar da Mista Trump ke alfahari da ita – katangar da ya fara ginawa tsakanin Amurka da Mexico. Kamfe din Biden ya kira wannan gini “?arnar ku?i”.

Ya kuma ce maimakon ?atar da ku?in da a ke yi a katangar, za a yi amfani da ku?in wajen tsaurara matakan tantancewa a iyakokin ?asar.

Kawo sauye-sauye a batutuwan wariyar launin fata da shari’a

Baya ga batutuwan cutar korona da tattalin arzi?i da sauyin yanayi – Mista Biden ya ce dole ne ya duba batun wariyar launin fata.
Ya yi al?awarin kafa rundunar da za ta taimaka wajen kawo sauyi a rundunar ‘yan sandan ?asar a kwanaki 100 na farko.

Kare auren jinsi ?aya

Ya yi al?awarin taimakawa masu auren jinsi ?aya da mutanen da suka sauya jinsi ta hanyar zuba ku?i a ?angarorin da ke kare wa?annan rukuni na mutane daga cin zarafi.

Sannan ya ce zai kawo ?arshen haramcin da aka ?ora wa mutanen da suka sauya jinsi na shiga aikin soja da dawo da hanyoyin wayar wa da yara kai kan batutuwan sauya jinsi a makarantu.

Ya kuma ce zai sa hannu kan dokar daidaito wadda za ta bai wa ‘yan ma?igo da ‘ya luwa?i damramaki.

Kwantarwa da ?awayen Amurka hankali

Sabon shugaban ya ce yana da shirin sasantawa da ?awayen Amurka da aka samu rashin jituwa da su kuma ya yi al?awarin “Amurka na nan tare da su”, inda ya ce dole ne Amurkar ta “nuna wa duniya a shirye ta ke ta sake jagorantar duniya kuma ta zama misali ga sauran ?asashe”.

Ya ce a ranarsa ta farko a babban ofishin shugaban ?asa ko Oval Office, zai aika sako ga ?awayen ?asar na NATO cewar |mun dawo kuma muna nan tare da ku”.

Duk da cewa ba Mista TRump ne shugaban ?asa na farko da ya matsawa ‘yan ?ungiyar NATO lamba ba wajen ?ara kasafin ku?i a kan tsaro, ya yi masu barazana a wasu lokuta da cewar zai janye daga gamayyar.

Exit mobile version