Ƙetare: An Naɗa Sabon Sarkin Kuwait Kwana Ɗaya Da Rasuwar Tsohon Sarki

Bayan rasuwar sarki Sheikh Sabah Al-Ahmed Al-Sabah na Kuwait majalisar masarautar ta nada dan’uwansa Yarima Sheikh Nawaf Al-Ahmed kwana daya tak da yin rasuwar.

Marigayi Sarki Sheikh Sabah al-Ahmed Al-Sabah ya rasu yana da kimanin shekaru 91 bayan fama da rashin lafiya tun a watan Yunin da ya gabata.

Sheikh Sabah Al-Ahmed Al-Sabah ya mulki kasar ta Kuwait na tsawon shekaru 14.

Ana sa ran Sabon Sarkin zai ɗora akan ayyukan ginin ƙasa kamar yadda marigayi ɗan uwan nashi ya faro.

A wani labarin makamancin haka jama’a a Jihar Kaduna dake tarayyar Najeriya na cigaba da zaman jiran ayyana sabon Sarkin Zazzau daga fadar gwamnatin jihar, bayan rasuwar tsohon Sarkin Zazzau Shehu Idris wanda ya ke tunkarar mako biyu da rasuwa.

Labarai Makamanta