Ƙetare: An Haramta Amfani Da Kafafen Sada Zumunta (Social Media)

Babban Daraktan Hukumar Sadarwar Uganda Irene Sewankambo ya umurci kamfanonin sadarwar kasar su dakatar da duk wata dama ta yin amfani kafafen sadarwa na zamani da hanyoyin tura sakonni ta intanet nan take.

Wannan umurni da aka bayar ranar Talata, na zuwa ne kasa da kwana biyu kafin zaben shugaban kasar da za a yi a ranar Alhamis.

Wani da ke da kusanci da hukumar sadarwar kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an fara bada umurnin ne a wani kiran waya da aka yi wa kamfanonin sadarwar cikin fusata da hassala.

Wannan umurni dai martani ne ga matakin Facebook na goge kafafen wasu maso goyon bayan gwamnatin kasar da ke neman juya akalar batutuwan da ke faruwa a kasar kafin zaben na gobe Alhamis.

Daga cikin dandalin kafafen da dakatarwar ta shafa akwai Facebook, Twitter, Whatsapp, Signal da Viber, kuma umurnin ya fara aiki a kansu tun a ranar Talatar.

Kuna ganin daukar wannan mataki ya dace?

Labarai Makamanta

Leave a Reply