?etare: An Gudanar Da Jana’izar Shugaba Deby

An gudanar da jana’izar Shugaba Idriss Deby Itno a yau Juma’a a N’Djamena babban birnin kasar kafin daga bisani aka binne shi a ainihin garin da aka haife shi.

An kashe shi ne a ranar Litinin lokacin da yake kan gaba wajen yakar ‘yan tawaye, wata kungiya da wasu jami’an soji suka kafa a 2016.

Shugabannin kasashen Mali da Guinea da kuma na Nijar sun isa kasar domin halartar jana’izar, ana sa ran shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai je N’Djamena duk da jan kunnen da ‘yan tawaye suka yi kan cewa shugabannin kasashen waje kar su halarci jana’izar saboda dalilin tsaro.

Bayan an kwashe awanni sojoji na bayani, limamin babban masallacin N’Djamena zai gabatar da addu’a ga marigayin.

Da kuma yamma ne za a dauki gawar marigayin zuwa Amdjarass, wani karamin kauye kusa da mahaifarsa da ke kusa da iyakar kasar da ta Sudan.

Shugaba Deby wani babban ?usa ne a wajen tsare-tsaren da suka shafi matsalar tsaro a yakin Sahel.

Dan gidan Idriss Deby Janar Mahamat Idriss Déby ne ya karbi jagorancin kasar karkashin kulawar majalisar sojoji ta kasar bayan mutuwar mahaifinsa, kuma a jiya Faransa ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin sojin.

?etare: An Gudanar Da Jana’izar Shugaba DebyJanar Deby mai shekara 37 ya ce za a shirya zabe karkashin tsarin dimokradiyya a kasar nan da watanni 18, sai dai yan adawa sun yi Allah-wadai da wannan shugabanci na shi, yayin da wani janar din soja ya ce da yawan sojoji ba sa murna da shirin mika mulkin.

Related posts

Leave a Comment