Cibiyar bincike kan al’amuran yau da kullum mai zaman kanta da ke kasar Australia (ASPI), ta ce gwamnatin China ta ruguza dubban masallatai a yankin Xinjiang.
Cibiyar ta wallafa rahoton ne a ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta sha wallafa bayanai kan irin cin kashin da kasar ke yi wa Musulmi da sauran kabilu marasa yawa a yankin na Xinjiang.
Cibiyar tace ta tattara bayananta ne ta wajen amfani da hotuna daga tauraron dan adam wadanda suka nuna cewar hukumomin kasar sun rusa Masallatai kusan 16,000 a yankin.
Hakan ya wakana ne a cikin shekaru uku da suka shige, kamar yadda sashen Hausa na RFI ya ruwaito.
Rahoton ya kara da cewar ko guda ba a taba wani wajen ibada na mabiya addinin Buddah ko kuma Mujami’u ba.
Zuwa yanzu sun rusa kaso daya bisa uku na wuraren ibadan Musulmai, musamman ma a biranen Urumqi da Kashgar da ke Xinjiang.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun dade suna zargin kasar China da garkame Musulmai ‘yan kabilun Uighur da Turkic su sama da miliyan daya.
An tsare su ne a wasu sansanonin da ke arewa maso yammacin kasar da aniyar tursasa musu barin addini da al’adunsu.