Ƙarshen Tika-Tika Tik: Buhari Ya Dakatar Da Magu Daga EFCC

Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar da ke yaki da masu yin babakere da tattalin arziki ta Nijeriya EFCC.

Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata.

A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba.

Kwamitin – karkashin jagorancin tsohon mai shari’a Ayo Salami – ya gayyaci Mr Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC.

Wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami’an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply