Tsohon Sanatan da ya wakilci shiyyar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa, Shehu Sani ya gargadi Amaechi ministan sufuri da kada ya kuskura ya kara kudin jirgin kasa daga Kauna zuwa Abuja zuwa Kaduna kamar yadda ya sanar.
Jaridar guidian ta wallafa cewa ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa za a kara kudin sufurin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja saboda yadda za a rage yawan wadanda za su rika shiga a dalilin annobar Korona.
” Akwai yiwuwar za a kara kudin jirgin kasa. Babban dalili kuwa shine, maimakon mutum 88 da kowanne tarago yake dauka yanzu mutum 40 ne kacal zai dauka saboda haka dole kudin ya karu, wato ya kusa rubunyawa ma.
Amaechi ya ce ba za su dauki wannan mataki ba sai sun shawarci shugaban kasa kuma ya basu amincewar ayi haka.
Sai dai kuma Sanata Shehu Sani ya kushe wannan mataki da gwamnati ke so ta dauka game da karin kudin sufurin jirgin.
” Yanzu fa titunan mu a Arewa sun koma hannu ‘yan bindiga, masu garkuwa da mahara. Jirgin ne mafita a gare mu, idan Buhari ya aminci aka kara kudin jirgin yaya mutane za su yi, domin nan ne kawai ya rage ake dan samu a bi.
Idan kudin shiga jirgin yayi tsada, yaya talaka zai yi da rayuwar sa, a wannan yanayi da ‘yan ta’adda, mahara da masu garkuwa.