Jam’iyya mai mulki ta (APC) ta daura laifin karin farashin man fetur kan jam’iyyar adawa ta (PDP) da gwamnatocinta na baya.
Jam’iyyar APC ta yi raddi ne ga PDP yayin data a soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin mai da na wutan lantarki lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin halin talauci.
APC ta ce gwamnatocin PDP da suka shude ne suka sace arzikin kasar nan ta hanyar biyan tallafin mai, kuma hakan ke sabbaba matsalan da ake fuskanta yanzu.
Kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
“Muna kira ga PDP ta ba ‘yan Najeriya mamaki ta hanyar yiwa shugabanninsu magana (yawancinsu dake kasashen waje) da suka sace mana arziki ta hanyar biyan tallafin mai, su dawo mana da su.”
“Karkashin shugaba Muhammadu Buhari, an daina samun karancin man fetur da layukan motoci.”
Mun kawo muku rahoton cewa Farashin man fetur ya karu zuwa N151.1 ga lita, a cewar kamfanin kasuwancin man fetur PPMC, wani sashen kamfanin man feturin Najeriya NNPC.
D.O Abalaka na kamfanin PPMC yace: “Ku sani cewa mun daura sabon farashin mai a shafin rubuta kudi.” “A yanzu, farashin man fetur PMS zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida ga lita.”
“Za’a fara aiki da sabon farashin daga 2 ga Satumba, 2020.”