Fadar Shugaban kasa tayi ?arin haske akan ?arin farashin man fetur, inda ta bayyana cewa ?arin ba zai shafi rayuwar talaka ba, domin ?ari ne da ya shafi masu abubuwan hawa da sauran masu amfani da na’urorin samar da wutar lantarki da sauransu.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a birnin tarayya Abuja.
Garba Shehu ya ce yawancin ‘yan Najeriya basu amfani da man fetur saboda haka ba zasu amfana da rashin tsadarsa ba, hakazalika tashin farashin ba zai shafesu ba.
Gwamnatin Buhari a farkon shekarar nan ta bayyana shirinta na cire tallafin mai tare da sauye-sauye a bangaren mai. Tun daga lokacin farashin ya dan sauka bisa ga saukar farashin danyar mai a kasuwan duniya sakamakon bullar cutar Korona.
Amma a watan Satumba, farashin ya fara hauhawa kuma hakan ya tayarwa ‘yan Najeriya hankali.
Wasu sun daurawa gwamnatin laifin bari farashin ya tashi duk da cewa ‘yan Najeriya na fama da tasirin annobar Korona a rayuwarsu.
Garba Shehu, ya ce babu adalci ace talakawa su cigaba da baiwa mazauna birni tallafi. “Shin ‘yan Najeriya nawa suka mallaki mota? ‘Yan Najeriya nawa ke amfani da Janareto a gidajensu da suke bukatar mai?
Shin akwai adalci manomi da makiyayi da talakawa, a rika daukan kudinsu ana biyan tallafin mai ga mazauna birni?”
“Saboda haka shugaban kasa na kokarin fito da komai fili ne kan lamarin.”