?arin Farashin Lantarki Ba Zai Shafi Talakawa Ba – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta yi fashin ba?i akan batun ?arin farashin wutar lantarki da aka yi, inda jama’a ke kokawa akan yadda ?arin ya zo babu zato babu tsammani, sai dai gwamnatin ta bayyana cewar ?arin ba zai shafi Talakawa ba ko ka?an, ?ari ne kawai da aka yi domin wa?anda ke cin gajiyar wutar lantarki da kaso 80 cikin 100.

Hukumar lura da hasken wutan lantarkin Najeriya NERC, ta karyata rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda jama’a ke biya yanzu a fadin tarayya, inda ta bayyana cewar labarin ba haka yake ba.

NERC a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa har yanzu bata bada umurnin kara farashin wuta ba kamar yadda kafafen yada labarai ke watsawa amma unguwannin masu kudi kawai aka karawa saboda wasu dalilai da suka shafi tattalin arziki.

Hukumar ta ce unguwannin da ke matsayin A, B, C, D da, E aka karawa farashin Kw/hr daga N2.00 zuwa N4.00 “Hukumar (NERC) ta samu labarin wallafe-wallafe da ake yadawa a kafafen yada labarai inda ake fadawa mutane cewa hukumar ta kara farashin wutan lantarki da 50%,.

“Kwastamomin dake matsayin D & E (wadanda ke samun wuta kasa da sa’o’i 12 a rana) ba ayi musu kari ba kuma har yanzu suna jin dadin tallafin gwamnatin tarayya.” “Amma bisa dokar EPRSA, an kara farashin wuta ga masu matsayin A, B, C, D da E daga N2.00 zuwa N4.00 sakamakon hauhawar tattalin arzikin Najeriya.”

Watanni hudu da suka gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin baiwa dukkan ‘yan Najeriya mitan wutan lantarki domin kawar da tsarin da ake kai yanzu na raba ‘Bill’ na kiyasi.

A takardar da aka saki ranar Laraba, shugaban hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), James Momoh, ya ce hakazalika shugaba Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan. Amma Momoh yace za’a togaciye “Talakawan” Najeriya daga karin farashin da za’ayi.

Shugaban NERC ya ce karin kudin ba zai shafi wadanda ake rabawa ‘Bill’ na kiyasi ba har yanzu har sai sun samu mita. Hukumar (NERC), ta sanar cewa za’a fara dabbaka karin farashin wutan lantarki fari daga ranar 1 ga Satumba, 2020.

Related posts

Leave a Comment