?addara Ce Ta Hanani Zama Shugaban Majalisa A 2015 – Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce bai zama shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015 ba saboda ba’a lokacin Allah ya tsara zai hau kujerar ba, domin komai na rayuwa yana tafiya ne bisa ?addara da hukuncin Ubangiji.

Shugaban Majalisar ya bayyana hakan ne a yayin taron bikin zagayowar ranar haihuwar shi Shekaru 62 da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai, Lawan ya ce duk da bai samu nasara a wancan lokacin ba, hakan bai hana shi yin aiki hannu da hannu da Bukola Saraki ba wanda ya yi nasara a wancan lokacin.

Jam’iyyar APC mai mulki ta zabi Lawan da Gbajabiamila a matsayin ‘yan takarar ta na shugaban majalisar dattijai da majalisar wakilai a shekarar 2015, sai dai dukkansu sun sha kaye a hannun ‘yan takarar da basu da goyon bayan uwar jam’iyya da fadar shugaban kasa.

Bukola Saraki ya lashe zaben kujerar shugaban majalisar dattijai a yayin da Yakubu Dogara ya lashe zaben zama shugaban majalisar wakilai a 2015.

Sau dai an shiga ‘yar tsama da zaman doya da manja a tsakanin tsofin shugabannin majalisar da fadar shugaban kasa da kuma uwar jam’iyyar a wancan lokacin, lamarin da ya tada ?ura sosai a wancan lokacin.

“Idan Za ku iya tunawa na nemi kujerar shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015, amma Allah cikin ikonsa bai kaddara zan sameta a wancan lokacin ba. “Ba lokaci bane, Allah ya riga ya tsara cewa Sanata Saraki ne zai hau kujerar a lokacin.
“Mun yarda da Allah, shi yasa muka yi aiki tare da shugabancin majalisa don kawowa jama’a cigaba har zuwa shekarar 2019, lokacin da Allah ya yi zan yi samu kujerar,” a cewar Lawan.

Related posts

Leave a Comment